Tattaunawa Da Umar M Shareef Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba. Akan Soyayyar Wata Nafara Waka

Tattaunawa Da Umar M Shareef Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba. Akan Soyayyar Wata Nafara Waka

A INA KA KOYI KARATUN AL’QUR,ANI ?

Ehh to gaskiya tin lokacin da na taso a gidan mu naga a na karatun addini sosai saboda haka nima ba’a barni a baya ba.

IZU NAWA KA HADDACE ?

Ehh, na haddace abin dana haddace amma ba dukkaba.

YA BATUN KARATUN ZAMANI ?

Ehh, karatun zamani ina yi yanzu haka ina KASU A nan Kaduna ina karanta political science.

ME YA JANYO HANKALINKA KA FARA WAKA ?

Sila dalili ne ya kawo in fara Rera Waka Sanadi na soyayya.
Akwai wata baiwar Allah da nagani ina sonta amma na kasa fada mata.

WACE WAKA CE WANNAN ?

Ehh, Amma Fah har yanzu ban Rera Wakar a Studio ba.

TOH YANZU KUNA TARE ?

Aa, Tun wannan lokacin da mukayi haka ban kara neman taba.

KANA BUGA KWALLON KAFA NE ?

Ehh, har yanzu inayin Training saboda kafin nafara waka har kudi a na biyana naje na buga kwallo.

KA TABA JIN CIWO A WAJEN KWALLO ?

Bazai huce shekara daya ba lokacin da na koma Training.

ME KE FARANTA MAKA RAI ?

Abun da ke faranta mini rai shine naje waje a mutuntani.

ME KE BAKAN TA MAKA RAI ?

Idan a ka wulakantani ko a nuna ni ba kowa bane.

DAN RERA MANA WAKAR KA DA KAFI SO ?

Bayan mutuwa ba komai daga kai sai halayyarka.

ME YASA KAYI WAKAR NAN ?

Ehh to abin da yasa nayi wakar saboda na kara tinawa mutane da kaina mutuwa.

AKWAI WAKAR DA KAKE SHIRIN SAKEWA ?

Ehh, gaskiya akwai wakoki masu yawa saboda ina tinanin kundi Zan fitar wanda yake dauke da wakoki 15. Sai Videos da bansan a dadin suba.

YAYA ALAQARKA DA ABDUL M SHARIFF ?

Abdul dan uwa na ne kuma yayana.

ANA KUSKUREN TANTANCEKU ?

Kwarai da Gaske ana kuskuren hakan kawaii idan mutum yace abdul naga fim dinka zance masa Nagode.

MATANKA NAWA ?

Matata guda daya sunan ta maryam sai yara na guda biyu ALIYU DA HAFSAT.

YAUSHE ZAKA YI TA BIYU ?

Kayi kasa-kasa da muryarka kawaii dai ban shirya bah.

WAI MARYAM YAHAYA BUDURWAR KA CE ?

Aa, maryam yahaya abokiya tace.

WANE ABINCI KAFI SO ?

To gaskiya nafison tuwo miyar kuka ko kuma tuwon shinkafa miyar Taushe.

WANE NE GWANIN KA A CIKIN MAWAKA ?

Ahh, Sadi Sidi Sharifai.

SU WAYE MANYAN ABOKAN KA A MAWAKA ?

Toh, Akwai Lilin Baba, Ado Gwanja, Ali Jita, Nura M Inuwa, Adam A Zango, da sauransu.

By Hausa

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *