Cikakken Tarihin Abba Kabir Yusuf Gida Gida

Abba ibn Muhammadu Kabir bn Dan makwayon Kano Yusuf bn Muhammad Bashir bn Galadiman Kano Yusuf bn Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi bn Sarkin Kano Ibrahim Dabo dan kabilar Sullubawa ne na kabilar Genawa ta Fulani, a bangaren uwa kuma yana da alaka da Walin Zazzau Sheikh Umarul.

Wali ibn Galadiman Zazzau Malam Ahmadu, kakarsa Zainab ibna Malam Saidu Limamin Huggalawa daga gidan Limamin Huggalawa ne a garin Bichi, kakarsa Khadijat Naja’atu tana da alaka da Gwani Mukhtar wanda shi ne jagoran Jihadin Fulani a Kanem- Daular Borno.

Haihuwarsa da Iliminsa

An haifi Abba ne a ranar 5 ga Janairu, 1963, a karamar hukumar Gaya ta Jihar Kano, ga Malam Kabiru Yusuf da Malama Khadijatul-Naja’atu.

Ya halarci makarantar firamare ta Sumaila tsakanin 1968 zuwa 1975.Daga nan ya halarci Makarantar Sakandare ta Gwamnati Dawakin Tofa kafin ya wuce Makarantar Sakandaren Gwamnati Lautai da ke Gumel, inda ya kammala a shekarar 1980.

Abba Kabir Yusuf ya kammala karatunsa na Difloma (ND) a fannin Injiniya na Kasa (ND) a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya ta Mubi a shekarar 1985, sannan ya yi Diploma na Higher National Diploma (HND) a Civil Engineering a Kaduna Polytechnic a 1989.

Daga nan ya sami shaidar kammala karatun digiri a fannin gudanarwa da kuma Master of Business Administration (MBA) a Jami’ar Bayero da ke Kano.SiyasaAbba shi ne kwamishinan ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri (jihar Kano), Abba ya tsaya takarar gwamna a zaben 2019 da aka gudanar a shekarar 2019, kuma gwamnan jihar Kano mai ci Abdullahi Umar Ganduje ya doke shi.

Abba ya kai karar kotu domin ya ce kansa a matsayin zababben gwamna, bayan da kotun ta yi watsi da karar.

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2024 Hausa Viral - WordPress Theme by WPEnjoy