Hadiza Gabon Tayi Hira Ta Musamman Tare da Dauda Kahutu Rarara – Ance Kan Rabawa Mata Motoci

Hadiza Gabon Tayi Hira Ta Musamman Tare da Dauda Kahutu Rarara – Ance Kan Rabawa Mata Motoci.

Assalamu Alaikum Waraha matullah, Nice Dai Taku Hadiza Gabon Yauma Muna Tare Da Babban Baƙon Mu Mai Suna Dauda Kahutu Rarara!

“Assalamu Alaikum Waraha matullah kamar yadda ta faɗa sunana Dauda Adamu wanda akafi sani da Dauda Kahutu Rarara.

IDAN UNGULU TA BIYA BUƘATA?

Okay ni kike tambaya wannan okay karina magana ne, ni bansan karin magana ba saboda ca ki kai inzo muyi Shira.

SUNAN KA RARARA?

Aa Sunana Dauda Adamu shi Rarara Nick Name ne.

TO YIMANA TAƘAITACCEN BAYANI KAN RAYUWAR KA?

Sunana Dauda Adamu wanda akafi sani da Dauda Kahutu Rarara an haife ni a garin Kahutu Ɗanja Local Government Katsina State, Nayi Primary na a Ɗanja da ƙyar na fara Secondary school aka kawo ni karatun Allo nan garin shi yasa ake cemin ƙolo.

Kuma a yanzu nine shugaban ƙasar ungiyar 13 × 13.

ITA 13 × 13 ƊIN ƘASA CE?

Ai kusan Duniyace ita ba ƙasa bace saboda ƙungiyace Talents da ba a taɓa yin irin ta ba, Duk wani mai basira yana ciki kamar Mawaƙi, Jarumi, dole dai sai ka ƙware zaka tsinci kanka a ciki .

MU KENAN BAMU KWARE BA KENAN?

Misali muke yi kuma ai, bamu zo kanki ba Hajiya Hadiza, saboda ita wannan ƙungiya mutun 13 suka haɗu aka buɗe ta.

KAI MAWAƘINE GAGARUMI KUMA NA SIYASA, ME YASA IYA SIYASA?

Saboda a cikin Al’ummar da Allah ya halicce mu a yanzu dole sai da siyasa, Tin da yanzu ba mulkin Soja ake ba duk inda zaka sai kayi Siyasa.

Wani misali kamar ni ai bana Acting amma Actor yana zuwa siyasa, Kin gane nufi na kuma bana Director amma Director yana zuwa harkar siyasa dole sai an yita.

A YAU MAN FETUR YA KAI 280 KUMA HAR YANZU KANA TALLATA WANNAN GWAMNATI?

Shine dai – daia, Wannan shine dai – dai.

MENENE DAI DAI A CIKI?


Da kin san abun da akeyi da man Fetur da kin siya Ɗari Uku yafi ace an siyar miki Naira ₦50.

KO ZAKA IYA MANA JAWABI AKAI?

Alhamdulilahi saboda kuɗi da Gwamnati take warewa ta bada don a siyar muku da Mai da araha, Yafi dacewa a ɗauki kuɗi ayi kamara Titi, Asibiti, Kuɗin Makaranta, da sauran su.

Kuma a wannan ƙasa tamu mai Albarka akwai talakan da bai da Mashin ko Mota ko Inji kai wani ko Keke bashi da shi, Saboda haka gwara a sai Mai da tsada ayiwa talakawa aiki.

Kuma duk duniya babu inda ake sai da Fetur da arahar Nijeriya, Amma kullum zagin Buhari ake meyayi shine yake sai da Mai kuma yanda kuka san Buhari har yanzu haka yake.

AMMA KUMA HAR YANZU TALAKA BAI DENA KUKA BA?

Ai kune ke saka shi kuka da maganganun ku, Akwai wanda yanzu idan kika je wajen sa kika ce Buhari baya kyautawa sai dai a ƙwaceki.

AN CE KANA RABAWA MATA MOTOCI, MENENE DALILI?

A su suke so, Su suke buƙata Ai.

A TO NIMA INA BUƘATAR MOTA DA IPHONE?

Ake bazan baki ba saboda kinfi ƙarfi Mota da iPhone, Saboda akwai Wadda tafara harkar fim ko wata sana’ar kinga sun buƙatar Mota su nake ba.

TO ME YASA SAI IYA MATA KAWAI KA KE BAWA?

Aa wanda ya faɗa miki haka yayi san zuciya ko kuma nace kin so kanki, Saboda ba maganar Mata ni duk wanda yake buƙatar wani abu ko Gida ko Mota ko mene idan naga zan iya zanyi.

AN CE KANA RIGIMA DA ABDULAMART, MENENE DALILI?

A ni ban taɓa rigima da Abdulamart ba gaskiya, Idan baki yarda ba yanzu ki kirashi ki tambaye shi kace masa mun taɓa rigima kiji.

AMMA ME YASA A SOCIAL MEDIA AKE GANIN KAMAR KUNA DABI?

A wannan kuma mutune ne saboda Abdulamart sai ya shekara bai ganni ba ga Nazifi Asnanic ma Abokina ne amma sai ya shekara bai ganni ba.

TO MENENE YAKE KAWO HAKA BAKWA HAƊUWA?

Saboda uziri yana min yawa sosai, Saboda kin ga bi Mawaƙine ni Manomi ne kuma ni Mafatauci ne ni ɗan Ball ne.

AMMA MUTANE DA DAMA SUNA GANIN KANA RIGIMA DASHI?

Mutane da suke ganin haka babu wanda yazu ya Tambaye ni menene mu’amalar ka da Abdulamart.

MENENE MU’AMALAR KA DA ABDULAMART?

Na farko Abdulamart Mai Kwashewa farko a ƙasa na yake saboda nine nake bada kuɗi ayi fim kuma nake bada kuɗi ayi bidiyon waƙa, shi dai aikin sa Producter Ni bana Gaba da Kowa.

DA KAI DA AISHA HUMAIRA SOYAYYA AKE KO AIKI?

Kin san mutane Aisha Humaira tana Office ɗina muna aiki, kuma yanda muke aiki a Office Ni na 1 wani na 2 ita ta 3 haka muke aiki.

Kuma yanzu duk inda kaga Aisha Humaira zaka gan ni shiyasa mutane masu saƙeƙe ko nace muatane irin Ku sune suke cewa muna Soyayya.

ZAƁI MUTUN ƊAN A CIKIN WAƳAN NAN

Muhammad Buhari KO Asiwaju Bola Ahmed Tinubu 6 ZAƁE ƊAYA ?

To Alhamdulilah Mai Girman Muhammad Buhari mai gira da Daraja.

ZAKA IYA FAƊA MANA ABU UKU AKAN MUHAMMADU BUHAR?

Ni dai tin ina ƙarami ake kiransa mai Gaskiya a Nijeriya kuma har yanzu ba’a sami madadin shi ba.

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2024 Hausa Viral - WordPress Theme by WPEnjoy