MASHA ALLAH Yau Munkawo Muku Jerin Jaruman India Goma (10) Da Suka Musulunta Da Kuma Takaitaccen Tarihin Su

By Real DBB Jan22,2024 #hotuna #labarai

MASHA ALLAH Yau Munkawo Muku Jerin Jaruman India Goma (10) Da Suka Musulunta Da Kuma Takaitaccen Tarihin Su.

An haife shi a matsayin ke bin addinin Hindu, daga bisani kuma ya karbi musulunci.

Ya sauya sunansa daga Dileep zuwa Rahman.

Mawakin indiya ne wanda ya lashe kyautar Oscar.

Mutun ne Kuma da tunaninsa ya karkata zuwa kin Manzan Allah, da farko, amma daga baya sai ya karbi musulunci ya Kuma zama karfaffan Imani Da Allah.

Abin da ya ce game da komawar sa musulunci ba abun mamaki bane Kamar yadda ake nunawa Mutanen mu sun kadaita saboda haka lokacin da wasu karance-karance na sufanci Suka Yi tasiri a kaina sai na Musulunta; Daga cikin wakokin sa da suka yi fice akwai Maa Tujhe Salam.

Ta fito ne daga cikin iyalan da akafi martabawa a kasar.

Marubuciya ce, ta Kuma Musulunta ne a 1999.

Ta sauya sunanta daga Madhavikkuty zuwa Kamala Surayya, bayan ta Musulunta.

Ta Musulunta ne bayan karanta wani littafi mai suna THE LOVE QUEEN OF MALABAR”. Littafin dai ya jawo cece-kuce a kasar.

Shahararren jarumin Fina-Finan Bollywood, Kuma mahaifin Sunny Deol, Bobby Deol, Esha Deol da Ahana Deol ko da yake ya karbi musulunci, amma majiyoyi sun ce baya d’abbaka shi.

Dalilin Musuluntar Sa shi ne, saboda ya auri Jaruma Hema Malini, a al’adar su mabiya addinin Hindu ba a auren mata biyu, to sai kuma soyayya ta shiga tsakanin sa da Hema har suka shirya auran juna a wancan lokacin, sai ya duba yaga ai addinin musulunci ya bayar da damar auren mata fiye da daya. sai ya Musulunta sannan suka yi aure tun a 1980 ya fito a fina-finai kamar Sholay da Jugnu.

Mawaki ne Kuma mai rubuta waka. ‘Da ne a wajan shahararren mawakin nan ilayaraja Bai jima da karbar musulunci ba.

Ya bayyana dalilin da ya sa ya Musulunta, ya ce Mahaifina rikakken mabiyin addinin Hindu ne, kuma yayi nisa wajen Camfe-Camfe ta yadda ko da gilashi ne ya fashe sai ya kira malamin duba.

Yace Dukkan iyayensa sunyi imani da camfi, to wata rana sai Mahaifiya ta mutu a hannuna bayan gajeriyar rashin lafiya, Nan na yi tunani nace ya aka yi haka, yanzu fa take numfashi, ta yanzu tana Ina? Anan na fahimci cewa ba Wanda zai karbi numfashinta Face Allah (SWA).

Furodusa ne Kuma daraktan Fina-Finan Bollywood Ya Musulunta ne saboda ya auri matar sa ta biyu Soni Razdan, kasancewa a addinin Hindu ba a auren mace fiye da guda daya.

To sai dai Kuma rahotanni sun ce duk da ya Musulunta baya d’abbaka addinin.

Mahesh Bhatt, mahaifi ne jaruma Pooja Bhatt da Alia Bhatt daga cikin Fina-Finan da ya shirya akwai Gumrah Da Duplicate.

Sharmila Tagore, ta Musulunta ne sakamakon auran mijin ta Masoor Ali Khan a shekarar 1969.

Ta sauya sunanta daga Sharmila Tagore zuwa Ayesha Sultana bayan Musuluntar ta ita da mijin ta, sun haifi ‘ya’ya uku Saif Ali Khan, Saba Ali Khan da kuma Soha Ali Khan.

Sharmila Tagore ta fito a Fina-Finan Bollywood da dama da suka yi fice Kamar Aradhana Wanda suka fito tare da Rajesh Khana.

Fitacciyar jaruma ce Fina-Finan kudancin indiya .

Ta sanar da Musuluntar ta ne a 2014, amma tun a 2010 ta karbi musulunci. Ta sauya sunanta zuwa MG Rehima, Mahaifin ta Hindu ne mahaifiyar ta Kuma kirista ce.

Hans Raj Hans, mawaki ne a indiya. Ya Musulunta ne a lokacin da yake kan hanyar sa ta zuwa Pakistan. A da Yana bin addinin Sikh ne, daga bisani kuma ya Musulunta.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *