Tattaunawa Tareda Sadiq Sani Sadiq.
WACECE BUDURWARKA A KANNYWOOD?
A Kannywood Babu A Yanzu Haka Budurwata Mataceh
MENE KE YAWAN SAKA DARIYA?
Abunda Yake Yawan Sani Dariya Gsky Sai An Bincika
MENE KE YAWAN BATA MAKA RAI ?
Abunda Yake Yawan Batamin Rai Shine Gulmar Wanii Ko Yin Maganar Wani Wanda Baya Wajen Wannan Dalilin Yasa Ba Kowa Nake Zama Dashi Bah.
WAYE AMININKA A KANNYWOOD?
Aminina a Kannywood Gaskiya Macece RAHAMA SADAU.
WACCE SANA’A KAFI SO ?
Sana’ar da Nafiso Bayan Harkar Film Itace Sayar Da Tsimmokara Wato Botik.
MENENE SIRRIN ZAMAN AURENKA ?
Sirrin Zaman Aurena Shine Babu Third-Party Tsakanina Da Matata Duk Abin Da Yazo Tsakanina da ita muke Tattaunawa Wala Mai Dadi Ko Marar Dadi.
WANNE IRIN SO KAKEWA MATARKA ?
Irin Son Da Baki Bazai Iya Fadaba Saidaii Zuciya.
YAUSHE ZAKA DAINA RAWA ?
Lokacin dazan daina rawa shine lokacin dazan daina film Domin idan ban daina film bah bazan daina rawaba
KA ZAMA DANGOTE KO KA ZAMA GWAMNAN KANO ?
Haba Hajiya Ya Ana Maganar Dangote Kice Wanii Gwamnan Kano Ga Gwamnan Africa Gaba Daya Aii DANGOTAN KAWAI 😂
AN TABA MARINKA KAGA WUTA ?
Kwarai Da Gaske Kakata Lokacin Danazo Mata Da Maganar Aurena Na Farko Lokacin Ina Kokarin Hada Kwalin Diploma sai Soyayyar Wata Yarinya ta debenii ko Sana’a bani da ita kawaii nazo mata da maganar Aure da Tayimin wani Mari saida naga taurari.
BUDURWA TA TABA BAKA KUNYA ?
Kwarai da gaske na taba zuwa hira Sainaga Suna Hira da wani saurayinta a cikin Mota kinsan Jos ana Sanyi naje na Zauna ina ta jiranka da suka gama shirar tana fitowa daga motar kawai saita shige gida Naji Zafi Sosai.
KA TABA SHAN MAGANIN TAURI ?
Nasha, ina kuma sha kuma bazan daina shaba Saboda Tsaro Kinsan Komai Na Iya Faruwa.
KANO KO JOS WANNE KAFI SO ?
Nafison Jos Saboda Anan Aka Haifenii Nanne Tushena Kano Kuma Anan Nasamu Daukaka Na Samu Kudii To Nafison Jos Fiye Da Ko Ina
SHEKARUNKA NAWA A DUNIYA ?
Inada Shekara 39 A Yanzu
WANNE YARE KAKEJI ?
Inajin Hausa Turanci Nakan Tsinci Larabci Kadan Kadan
YI MANA LAYI DAYA NA LARABCI ?
Sabahul khair Sabahul Nurr
YA KAKE FARAUTA ?
Lokacin Da Nake Farautar Bawaii Wani Yanayi Bane Nadaban Kawaii Dai Ajene A Kamo Nama A Lokacin
DA WA KAFI SO A HADAKA RAWA A FIM ?
Rahama Sadau Domin Aminiya Tace Kawa Tace
WANE NE UBAN GIDANKA A KANNYWOOD ?
A Kannywood Banida Uban Gida Saboda Babu Wanda Ya Koyamin Sana’ar Da Nakeyi Amma Akwaii Wasu Mutane Da Nake Kallansu Da Kima Saboda Na Zauna A Karkashin Su Amma Basu Suka Koyamin Sana’ar Da Nakeyi Ba Akwaii
1= BELLO MUHAMMAD BELLO
2= ALI NUHU
3= MALAM AMINU SAIRA
4= UMAR UK
5= ADAM A ZANGO
Wannan Sune Mutanen Da Nake Kallansu Da Kima A Kannywood Amma Banida Ubangida
KANA SA GWANJO ?
Sosai ma Dayake Na Sayar Da Gwanjo Kuma Ni Nafison Gwanjo Fiye Da Sabon Kaya Sabida Idan Kasa Gwanjo Har Ya Mutu Ba Lallai Kaga Wani Yasa Irinsa.