Tattaunawa Da Ado Gwanja Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba. Da Wahalar Da Yasha
“Mahaifina ne ke yiwa sarkin Kano shayi – Ado gwanja”
SU WAYE MANYAN ABOKANKA A KANNYWOOD ?
A bangaren fim dai bani da abokin daya wuce DAN AUTA. Don mun fara abota dashi tin kafin mu shigo fim ko tare dashi muka sha wahalar Allah ne yabashi dama kafin ta same ni. Amma a bangaren WAKA Umar M Sharif, Usaini Danko, Hamisu Breaker, Da sauransu..
TAMBAYA DA KA GAJI DA AMSAWA ?
Toh ai Bani da wata tambaya da na gaji da amsawa don har Yanzu ba’a yimin tambayar da ta gajiyar dani ba.
WACE KALAR MACE KAFI SO ?
Wacca na Aura.
YA KALAR TA TAKE ?
Farace tsayinmu daya bata da kiba kuma ba siririya bace.
MEYE YAKE SAKA FARIN CIKI ?
Abun da yake sani farin ciki shine shira da iyali na.
INA KA FI SON ZUWA A DUNIYA ?
Gaskiya Ina son zuwa kasashe da yawa kamar Paris, Germany, Italy, Europe, india Abu Buwan mu Suke Da Yawa.
ME YASA KA FI SON TURAI ?
Ahh Yadda Muka dauka mu mutanen mu idan ka tushe tinanin ka ka Tsaya waje daya baka da wanii abu na ci gaba toh xaka tsaya ne a wannan gurin idan daukaka ce idan wata dama ce a nan zaka gama idan baka bude tunanin kaba.
WACE CE BUDURWAR KA TA FARKO ?
Idan Na fada zataji haushi.
WACE SANA’A ZAKA YI DA BA KA WAKA ?
Toh mu sana’ar gidan mu shayi ce shayi muke yi kusan dai ko sarkin KANO zai sha shayi kafin mahaifinmu ya rasu to gurin mu ake zuwa a karbar masa shayi ko kuma mu dauka mu kai masa.
YAUSHE ZAKA KARA AURE ?
Gaskiya ba muyi haka da ita ba sabo da ina ma tsoranta a takaice.
MIJIN TACE NE KENAN ?
Ai ni kam tace ne ma
‘YA’YA NAWA KA KE SO ?
Toh kinsan Manzon Allah Yace kuyi aure domin ku ha yayyafa sabo da ranar gobe kiyama nayi alfahari daku.
“Ba waii Limit ne dani na ‘ya’yan da zan Haifa bah sabo da In Allah ya kawo ina lale dasu sabo da bakasan a inna arzikin naka yake ba. toh amma idan tsarina ne banason na huce 2,3.
ME YASA KAKE SON YIWA MATA WAKA ?
Sabo da sune iyayen Biki kuma idan akayi Biki idan har kida yakai sune kadai suke rawa su bawa waje nishaɗi.
ZAKA BAR ‘YA’YAN KA SU GAJE KA ?
Ehh, kinsan ai Allah ne yake kaddara wa mutum me zaiyi ida to in da na daka ta mahaifina nima shayi zanyi to kai kana lissafa inda xakayi ne in Allah ya lissafo maka inda ya fiye maka nan saikayi don kafin Ni a wannan masana’antar a gidan mu Yayana aka fara ji babban wammu SA’EDU GWANJA Wanda shine ya shuga banci kannywood din gaba daya ya zama shugaban ta Lokacin 2007 shi kansa baiyi tunanin zanzama haka a cikin Sana’ar bah sabo da xaije yayi Sana’ar sa ne ya dawo ya same ni a kasuwa mutafi gida tare idan kuma baya nan in tafi kallo sabo da bai San ina zuwa kallon bah.
MENE SHAWARARKA GA MATASA ?
Matasa shawara ta a gare su daya ce Matuka ina son naga matashi kamar ni bawai irin sana’a ta ba kowa yana da inda yake so yaje. Ka zama mai kirkirar abu wanda zaka dauki hankalin al’umma ya taho gare ka. karka yarda ka zauna jiran wani zai baka bayan shima wannan mai bakan jira yake Allah ya bashi. To idan ka zama mai kirkirar abu a kanka ya zamo matasa suna da Sana’a da yawa. To ko banza za’a ragewa gwamnati takardun da suke gabanta na neman aiki.
MUN GODE DA BAMU LOKACI DA KAYI